in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu dakarun sojin Najeriya sun bace bayan da wasu mahara suka yi musu kwantan bauna
2018-07-16 09:27:22 cri

Rahotanni daga arewa maso gabashin Najeriya na cewa, wasu da ake zaton mayakan kungiyar Boko Haram ne sun yiwa dakarun sojojin Najeriya kwantan bauna a kauyen Boboshe, dake yankin Bama ta jihar Borno, lamarin da ya sabbaba bacewar wasu daga sojojin.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ya bayyana cewa sojojin na tafiya ne cikin wani jerin gwanon motoci kimanin 8, lokacin da 'yan bindigar suka far musu da sanyin safiyar ranar Asabar.

Wata majiya ta bayyana cewa, a kalla sojoji 70, ciki hadda manyan hafsoshi a kalla 5 ne ba su koma sansanin su ba, bayan harin da aka kaddamarwa tawagar ta su. An ce dandazon masu dauke da makaman da suka far wa sojojin sun haura mutum dari. Kuma bayan farmakin, motocin sojin 3 cikin 11 ne suka koma zuwa sansanin su dake kauyen na Boboshe.

Ana dai hasashen cewa, maharan da suka far wa sojojin gyaron 'yan Boko Haram ne da aka raba da maboyar su dake sassan dajin Sambisa, da yankunan tafkin Chadi.

Wani ganau mai suna Yusuf Mustapha, ya shaidawa majiyar mu cewa, tuni mazauna kauyen da lamarin ya faru suka tsere domin kaucewa abun da ka je ya zo. Kawo yanzu dai rundunar sojojin Najeriyar ba ta fidda wata sanarwa game da harin a hukumance ba.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China