Kakakin rundunar Texas Chukwu, ya musanta rahoton da cewa ba gaskiya ba ne, inda ya ce babu wani soja da ya bata yayin kwanatar baunan da ta auku a yankunan Kwakwa da Chingori na karamar hukumar Baman jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar.
Kakakin ya ce suna zargin mayakan Boko Haram da yunkurin kai wa sojoji hari a wadancan yankunan sanadiyyar kafewar da motocinsu suka yi saboda yanayin hanya.
Ya kara da cewa, 'yan ta'addan sun kuma yi yunkurin tafiya da motocin nasu, amma kuma sojojin tare da taimakon takwarorinsu na sama, sun yi nasarar fatattakar mayakan. (Fa'iza Mustapha)