in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta damke mayakan Boko Haram 22
2018-07-19 11:20:35 cri
Kimanin mayakan Boko Haram 22 aka damke a Najeriya bayan wani samame da jami'an 'yan sandan kasar suka kaddamar a maboyar mayakan.

Hukumomin 'yan sandan sun tabbatar da cewa mutane 8 daga cikin wadanda aka damke din ana zargin suna da hannu wajen sace 'yan makarantar sakandaren 'yan mata ta garin Chibok sama da 200 da aka yi garkuwa dasu a shekarar 2014 a jahar Borno a arewa maso gabashin kasar.

Wadanda ake zargin sun hada da wasu manyan kwamandojin kungiyar ta Boko Haram su 3, da mutane biyu dake samar musu kayayyakin bukatun yau da kullum da kuma mayaka kimanin 17.

An samu nasarar cafke su ne a lokacin da tawagar 'yan sandan musamman da aka tura yankin suka kaddamar da samame kan mayakan a shiyyar arewa maso gabashin kasar makonni biyu da suka wuce.

Dukkan wadanda ake zargin sun amsa laifin kaddamar da hare haren a matsayin mayakan Boko Haram, wanda ya hada da kaddamar da hare hare kan wasu garuruwa da shirya kai hare haren kunar bakin wake sama da sau 50 a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, kamar yadda Damian Chukwu, kakakin hukumar 'yan sandan jahar Borno ya tabbatar da hakan.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China