in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojoji sun kashe mayakan Boko Haram 5 a Najeriya
2018-07-02 20:34:44 cri
Rahotanni daga Najeriya na cewa, dakarun kasar sun yi nasarar kashe mayakan Boko Haram 5, yayin wani hari da suka kaddamar ranar 30 ga watan Yunin da ya gabata a kauyen Anadawa dake arewacin jihar Borno da nufin kakkabe gyauron 'yan ta'adda a yankin arewa maso gabashin kasar.

A wani labarin kuma, sojojin sun yi nasarar dakile wani hari da 'yan ta'addan suka yi shirin kaiwa jiya Lahadi a yankin Bama dake jihar ta Borno.

Sai dai Kakakin sojojin kasa na Najeriya Birgediya janar Texas Chukwu ya bayyana cewa, fararen hula guda biyu sun gamu da ajalinsu wasu uku kuma sun jikkata lokacin da sojojin ke kokarin dakile wannan hari.

Chukwu ya ce, mayakan Boko Haram 32 sun mika wuya a wasu cibiyoyin Soja dake jihar Borno, inda ake tantance su kafin a mika su ga hukumomin da suka dace. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China