Da yake tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Larabar nan, kakakin rundunar Texas Chukwu, ya ce da yawa daga 'yan ta'addan sun tsere da raunukan bindiga, bayan dauki ba dadi da sassan biyu suka gwaza da yammacin ranar Litinin.
Chukwu ya ce dakarun Najeriyar sun gudanar da aiki ne a yankin da hadin gwiwar kasar Kamaru. Kaza lika dakarun sojin sun gano tarin harsasai da mayakan Boko Haram ke amfani da su.
A ranar 15 ga watan Mayu ne dai Sojojin Najeriyar suka kaddamar da wani aikin soji na watanni 4, a wani mataki na kakkabe gyauron mayakan na Boko Haram daga dukkanin yankunan tabkin Chadi.