in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An hallaka mutane 6 a harin kasuwar Iware dake jihar Taraba
2018-07-18 20:49:51 cri
'Yan kasuwa 6 sun rasa rayukan su, yayin da wasu mutane a kalla 17 suka ji raunuka, sakamakon wani harin da wasu suka kaddamar da wukake a kasuwa Iware, dake yankin Ardo-kola na jihar Taraba.

Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar wannan lamari a ranar Talata. Da yake karin haske game da hakan, kakakin rundunar David Misal, ya ce mahukuntan jihar sun ba da umarnin rufe kasuwar ta Iware. Kuma tuni aka fara gudanar da bincike domin gano musabbanin aukuwar lamarin.

Kawo yanzu dai ba a kama kowa ba, sai dai 'yan sanda na ci gaba da nazari tare da tattara bayanai. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China