Gwamnan jihar Aminu Belllo Masari, ya shaidawa manema labarai jiya cewa, sama da gidaje 500 ne suka lalace a yankin karamar hukumar Jibiya dake jihar.
Aminu Masari, ya ce gwamnati ta tsugunar da wadanda iftila'in ya shafa a wata makarantar firamare dake yankin.
A cewarsa, ya sanar da gwamnatin tarayyar kasar game da iftila'in, ya na mai jadadda cewa tuni hukumar bada agajin gaggawa ta kai manyan motoci 13 shake da kayakin jin kai da za a raba ga mutanen.
A nasa bangaren, shugaban kasar Muhammadu Buhari, ya bayyana damuwa da bakin ciki game da aukuwar iftila'in da ba a taba gani ba a jihar Katsina da ma wasu sassan kasar. (Fa'iza Mustapha)