in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Katsina: Adadin wadanda suka rasu sakamakon ambaliyar ruwa sun kai mutum 52
2018-07-18 20:45:13 cri
Rahotanni daga tarayyar Najeriya na cewa, adadin mutanen da suka rasu, sakamakon ambaliyar ruwa a jihar Katsina dake arewa maso yammacin kasar ya kai mutum 52. Kaza lika a kalla mutane 24 sun samu raunuka, an kuma garzaya da su asibiti sakamakon hadurra daban daban, da ambaliyar ruwan ta haifar a kauyuka 5 na karamar hukumar Jibia dake jihar.

Da yake tabbatar da hakan, shugaban hukumar ba da agajin gaggawa na jihar ta Katsina Aminu Waziri, ya ce an samo gawawwakin mutane 52 daga kauyuka 5, kana ana ci gaba da neman wasu mutanen 20. Jami'in ya ce an zakulo wasu gawawwakin ne daga karkashin gine gine da suka fadi sakamakon mamakon ruwa da ya haddasa rushewar gidaje masu yawa. Yayin da kuma aka samo gawawwakin wasu su 24 a wasu kauyuka 2 dake jamhuriyar Nijar mai makwaftaka da yankin, bayan da ruwa ya yi awon gaba da su.

Sama da gidaje 500 ne suka lalace, kana mutane kusan 5,000 suka rasa matsugunnansu, sakamakon wannan ibtila'i da ya auku. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China