in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Najeriya sun kashe mayakan Boko Haram 22
2018-07-16 21:31:35 cri
Rahotanni daga Najeriya na cewa, sojojin kasar sun yi nasarar kashe a kalla mayakan Boko Haram 22 yayin wata musayar wuta a karshen mako a yankin Bama na jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar.

Wata sanarwa da sojojin suka raba manema labarai, ta bayyana cewa wasu mayakan kungiyar da dama sun arce da harbin bindiga a jikinsu. Haka kuma wani soja da jami'i guda 1 sun samu raunuka, inda suke karba magani a cibiyar lafiya ta soja.

Sanarwar ta kara da cewa, yanzu haka ana kokarin ganin an kama 'yan ta'addan da suka gudu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China