in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da sabon jirgin kasan birnin Abuja dake Najeriya
2018-07-13 10:21:47 cri
A jiya ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da tsarin jirgin kasan fasinja mai sauki da zai rika zirga-zirga a birnin Abuja, fadar mulkin Najeriya. Jirgin wanda kasar Sin ta taimaka wajen ginawa, shi ne irinsa na farko a yammacin Afirka, kuma bankin shige da fice na kasar Sin ne ya ba da wani kaso na kudin aikin

A jawabinsa yayin bikin kaddamarwar, shugaba Buhari ya bayyana aikin a matsayin mai muhimmanci a tarihin kasar. Ya kuma bayyana tabbacin cewa, jirgin kasan na zamani zai taimaka wajen bunkasa tattalin arziki da rayuwar mazauna birnin.

A nasa jawabin manajan gudanarwa na kamfanin CCECC da ya kula da aikin Kong Tao ya ce, daga yau Jumma'a matafiya za su rika zirga-zirga kyauta har na tsawon wata. Ya ce, taragu uku da jirgin ke amfani da su a halin yanzu za su iya daukar sama da fasinjoji 300 a lokaci guda. Ana kuma sa ran a kalla fasinjoji 1,000 za su rika zirga-zirga a kowa ce rana.

Ya ce, layin jirgin mai tsawon kilomita 45, zai rika zirga-zirga ne a sassan birnin. Sabbin sassan da aka kaddamar a jiya, wani bangare ne na tsarin jirgin kasan birnin mai tashoshi 12 da ofisoshi 21 da gadoji 13 da kwalbatoci 50 da hanyoyin tafiyar jama'a guda 9.

An kuma tsara hanyar jirgin da yadda zai hade da babban layi na kasa a wurare guda biyu, haka kuma za su iya hadewa da layin jirgin kasan da ya hade yankin arewacin kasar

Bayan bikin kaddamarwar an kuma yi gwajin jirgin na watanni uku, inda mazauna birnin na Abuja za su fara cin gajiyar sabon tsarin sufurin kasar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China