in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a bude dandalin kafofin watsa labarai na BRICS a Afirka ta kudu
2018-07-17 20:25:30 cri
A gobe ne ake sa ran za a bude dandalin kafofin watsa labarai na kasashen BRICS karo na uku a birnin Cape town na kasar Afirka ta kudu mai taken "Hadin gwiwar kasashen BRICS a fannin kafofin watsa labarai.

Abubuwan da ake fatan tattaunawa a taron da zai gudana daga goben 18- 19 ga watan Yuli, sun hada da rawar da kafofin watsa labarai ke takawa wajen karfafa kawancen kungiyar, da karfafa sabon hadin gwiwar kafofin watsa labarai a kasashen na BRICS da ma hadin gwiwar kafofin watsa labarai tsakanin BRICS da Afirka.

Dandalin wani bangare ne na taron kolin kasashen BRICS karo na 10 da za a gudanar daga ranar 25-27 ga watan Yuli a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu, inda za a canja shugabancin kungiyar a shekarar 2018. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China