in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabon jakadan Sin dake Afirka ta Kudu: kasashen BRICS kasashe ne da suka sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya
2017-08-25 14:00:08 cri
Jiya Alhamis, sabon jakadan Sin dake kasar Afirka ta Kudu Lin Songtian ya gudanar da taron manema labaru karo na farko bayan da ya kama aiki.

A yayin taron manema labaran, Lin Songtian ya bayyana cewa, a matsayinsa na sabon jakadan Sin dake Afirka ta Kudu, zai himmatu wajen zurfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni dake tsakanin Sin da Afirka ta Kudu, kana yana goyon bayan rawar da kasar Afirka ta Kudu ke takawa na jagoranci a nahiyar Afirka a fannonin samun bunkasuwa da kiyaye zaman lafiya da tsaro a nahiyar Afirka, zai kuma yi kokarin raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa matsayin dangantakar da za ta jagoranci bunkasuwar dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka.

Game da ganawa ta 9 a tsakanin kasashen kungiyar BRICS da za a gudanar a birnin Xiamen, Lin Songtian ya bayyana cewa, tun daga shekarar 2006 zuwa 2016, an samu babban ci gaba kan hadin gwiwar dake tsakanin kasashen kungiyar BRICS.

A fannin tattalin arziki, yawan tattalin arzikin kasashen kungiyar BRICS a wadannan shekaru 10 ya karu daga kashi 12 zuwa kashi 23 cikin dari bisa na dukkan duniya, yawan cinikinsu ya karu daga kashi 11 zuwa kashi 16 cikin dari, kana jarin da aka zuba ga kasashen waje ya karu daga kashi 7 zuwa kashi 12 cikin dari, kasashen kungiyar BRICS sun samar da kashi fiye da 50 cikin dari na bunkasuwar tattalin arzikin duniya a wadannan shekaru 10, a don haka sun zama muhimman kasashe da suka taimaka ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China