in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta taimakawa kasashen Afirka wajen shigar da na'urorin kama shirye-shiryen talibijin na zamani a kauyuka dubu 10
2018-07-06 19:33:07 cri
A yau Juma'a, a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa, wani dan jarida ya tambayi Mr. Lu Kang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin cewa, ina halin da ake ciki game da aikin shigar da na'urorin kama shirye-shiryen talibijin na zamani a kauyuka dubu 10 na kasashen Afirka, wannan yana daya daga cikin matakan tallafawa kasashen Afirka da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya sanar a yayin taron shugabannin kasashen Sin da na Afirka na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka FOCAC da aka shirya a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu a watan Disamban shekarar 2015? Lu Kang ya bayyana cewa, tuni aka kaddamar da aikin a watan Agustan bara, kuma yanzu haka ana aikin shigar da irin wadannan na'urori a kauyuka dubu 10 na kasashen Afirka 25, inda kwalli ta fara biyan kudin sabulu a bangaren rayuwar mazauna kauyukan.

Lu Kang ya ce, mukasudin aiwatar da wannan aiki shi ne inganta zaman rayuwar jama'ar wurin, da kuma kara yin cudanyar al'adu da fahimtar juna tsakanin al'ummomin kasashen biyu. A kwanan baya, a yayin bikin kaddamar da aikin da aka shirya a wani kauyen kasar Zambiya, daliban makarantar firamaren kauyen sun kalli wasu gasannin kwallon kafa na duniya da ake gudanawar a kasar Rasha ta talibijin da kamfanin kasar Sin ya samar musu.

Lu Kang ya kara da cewa, a yayin taron koli na Beijing na dandalin FOCAC da za a shirya a watan Satumban bana, za a gabatar da sabon shirin bunkasa dangantakar huldar abokantaka irin ta hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka daga dukkan fannoni. Muna fatan mu da abokai 'yan uwanmu na kasashen Afirka za mu kara yin hadin gwiwa domin samun nasara da neman ci gaba tare, ta yadda jama'ar kasashen Sin da Afirka za su samu karin sakamako mai gamsarwa. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China