Yayin taron da zai gudana tsakanin ranekun 28 zuwa 29 ga watan nan na Yuni a birnin Durban, ana sa ran mahalartansa za su tattauna game da harkokin tsaro.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Geng Shuang ne ya tabbatar da hakan a yau Litinin, yayin taron manema labarai da aka saba shiryawa a nan birnin Beijing. (Saminu Hassan)