in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babbar jami'ar MDD ta danganta matsalar sauyin yanayi da tabarbarewar tsaro
2018-07-12 10:02:33 cri
Mataimakiyar babban sakataren MDD Amina Mohammed ta bayyana alakar dake tsakanin matsalar sauyin yanayi da zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, kana ta bukaci a dauki matakai na hadin gwiwa don a yiwa tufkar hanci.

Amina Mohammed, wacce ta dawo daga halartar shirin wanzar da zaman lafiya na hadin gwiwa tsakanin MDDr da kungiyar tarayyar Afrika a Sudan ta kudu, Nijer da Chadi, inda ta buga misali da tafkin Chadi.

Ta ce koma bayan harkokin tattalin arziki da tabarbarewar ayyukan noma sun haifar da karancin ayyukan dogaro da kai a yankunan. Sakamakon koma bayan tattalin arzikin ya jefa rayuwar al'umma cikin matsanancin hali, musamman matasa, inda suke fuskantar barazanar yaduwar akidu na masu tsattsauran ra'ayi kuma hakan yana baiwa kungiyoyin 'yan ta'adda irinsu Boko Haram damammakin daukar matasan aiki domin gudanar da ayyukan ta'addanci.

Amina wacce 'yar asalin Najeriya ce ta bayyana cewa, rikicin Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya da makwabtan kasashen Kamaru, Chadi da Nijer ya tilastawa mutane kusan miliyan 10 barin mahallansu, da kuma lalata muhimman kayayyakin more rayuwa da suka hada da asibitoci, makarantu da kasuwanni, da lalata gidaje da ayyukan noma. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China