A cewar wani rahoto da ofishin kula da harkokin jin kai na MDD ya fitar a makon da ya gabata, tun daga farkon watan Yuni, kusan al'ummar kasar miliyan guda ne suka rasa matsugunansu saboda rikici tsakanin al'ummomi dake kara ta'azzara.
A cewar rahoton, mutanen da yawansu ya kai dubu 793 ne suka rasa matsugunansu a yankin Gedeo, yayin da wasu a kalla dubu 185 suka rasa nasu a yankin yammacin Guji na kasar.
Mataimakin Firaministan kasar Demeke Mekonnen, wanda ya kai ziyara tare da wasu shugabannin yankuna, ga wasu daga cikin 'yan gudun hijirar a jiya Juma'a, ya jaddada bukatar gaggauta hada karfi da karfe tsakanin gwamnatin tarayya da na yankuna, domin tsugunar da mutanen da abun ya shafa a yankunan Gedeo da yammacin Guji.
Ofishin na MDD ya ce, yawan wadanda suka yi gudun hijira cikin kankanin lokaci ya haifar da matsananciyar matsalar jin kai. Kuma yayin da Gwamnati da al'ummomin da suka karbi 'yan gudun hijirar ke samar musu da galibin kayayyakin jin kai, akwai bukatar samun karin tallafi yayin da bukata ke karuwa. (Fa'iza Mustapha)