in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in MDD ya yi Allah wadai da harin da aka kaddamar kan tawagar firaiministan Habasha
2018-06-24 15:31:17 cri
Sakatare janar na MDD Antonio Guterres ya yi Allah wadai da harin da aka kaddamar kan taron gangamin da firaiministan kasar Habasha Abiy Ahmed ya halarta.

A wata sanarwa ta bakin babban sakataren MDD Stephane Dujarric ya ce, Guterres ya yi matukar nuna damuwa bisa samun labarin harin, kana ya yi Allah wadai da faruwar lamarin.

Sanarwar ta kara da cewa, babban sakataren ya bayyana cikakken goyon bayansa ga gwamnati da al'ummar kasar Habasha.

Maharin wanda ya sanya kayan 'yan sanda a jikinsa, ya jefa gurneti ne a taron gangamin da aka gudanar a Addis Ababa a jiya Asabar, jim kadan bayan da firaiministan kasar ya kammala jawabi.

Rahotannin sun bayyana cewa, mutum guda ya mutu kana sama da mutane 100 kuma sun jikkata a lokacin da aka samu turmutsitsi a sanadiyyar harin. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China