in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Habasha da Eritrea sun amince da hadin gwiwa wajen hada hadar sufuri
2018-07-09 19:48:08 cri

Mahukuntan kasashen Habasha da Eritrea, sun amince da maido da hulda a fannin sufuri, inda a yanzu za su ci gaba da sufurin jiragen sama a kasashen juna, kana Habasha da ba ta da tashar jiragen ruwa, za ta rika amfani da tashar ruwan Eritrea wajen dakon kayayyakin ta na cinikayya da kasuwanci.

Da yake tabbatar da hakan a jiya Lahadi, cikin wata sanarwa bayan isar sa kasar Eritrea, firaministan Habasha Abiy Ahmed, ya ce sufurin jiragen sama tsakanin kasashen biyu, da amfani da tashar ruwan Eritrea, matakai ne da za su ba da damar musaya tsakanin kasashen biyu.

Ahmed ya kara da cewa, shi da shugaban kasar Eritrea Isaias Afwerki, sun amince su sake bude ofisoshin jakadancin kasashen su a kasashen juna.

An dai yada sanarwar da firaminista Abiy Ahmed ya katanta kai tsaye ta kafafen talabijin na Habasha da na Eritrea.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China