in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in MDD yace babu lokacin mike kafa game da cimma ajandar 2030
2018-07-10 10:27:23 cri
Babban jami'in kula da fannin tattalin arziki da walwalar jama'a na MDD Liu Zhenmin, yace a halin da ake ciki yanzu babu wani lokaci na mike kafa, ya furta hakan ne a lokacin da yake gabatar da rahoto game da irin cigaban da aka samu dangane da ajandar samar da dawwamamman cigaba.

A cikin shekaru uku tun bayan da shugabannin duniya suka mayar da hankali wajen kawo karshen matsalolin talauci da yunwa, kasashen duniya suke cigaba da yin aiki tukuru wajen aiwatar da shirin muradun cigaban domin samun kyakkyawan sakamako, inda a wannan mako wasu rahotanni da dama suka nuna cewa an samu cigaba, Liu ya bayyyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga babban taron MDD game da shirin samar da dawwamamman cigaba wanda za'a kammala a ranar 18 ga wannan wata, taron wanda zai kasance a matsayin jigon tabbatar da nasarar shirin na (SDGs).

To sai dai kuma, tun a shekarar 2000, a kasashen kudu da hamadar Saharar Afrika, yawan matuwar mata masu juna biyu ya ragu da kashi 35 bisa 100 kana mutuwar kananan yara 'yan kasa da shekaru 5 ya ragu da kashi 50 bisa 100. A kudancin Asiya kuwa, barazanar yin auren wuri ga yara mata ya ragu da kashi 40 bisa 100.

Yac e sauye sauye da za su tabbatar da samun dawwamamman cigaba da ingantaciyyar al'umma ya ta'allaka ne da yadda ake tafiyar da dunbun albarkatun da ake da su, Liu ya kara da cewa, a halin yanzu akwai kasashen duniya kimanin 108 wadanda suka bullo da shirye shiryen samar da dawwamamman cigaba. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China