in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala taron hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD da kudure-kudure kan Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da Syria
2018-07-07 17:16:01 cri
Hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD, ta amince da wasu kudure-kudure a ranar karshe na taronta karo na 38, wadanda suka hada da tura tawagogi 2 na kwararru zuwa Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo da wata zuwa Syria.

Sanarwar da aka fitar a karshen taron da aka fara daga ranar 18 ga watan Yuni zuwa 6 ga watan Yuli, da sannan ne Amurka ta sanar da shawararta ta janyewa daga hukumar, ta bukaci shugaban hukumar ya tura tawagogi 2 na kwararru kan hakkokin bil adama zuwa Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

Hukumar ta dorawa kwarrarun nauyin ba ta rahoto kan yadda kasar ke aiwatar da shawarwarin da kwarrrun da aka tura a baya suka ba ta, game da yaki da cin mutunci da daukar matakan sulhu.

Da farko, hukumar ta amince da wani kudurin kare hakkin bil adama a Syria, bisa kuri'ar da ta kada, da ya samu na amincewa 26, da na kin amincewa 5, yayin da mambobi 15 suka kauracewa kada kuri'ar, wanda ya bukaci dukkan bangarorin dake rikici a kasar, su yi biyayya ga dokokin kare hakkokin dan Adam da ta agajin jin kai na kasa da kasa. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China