Hare-haren wadanda aka kaddamar a ranakun Litinin da Talata a shiyyoyin arewa maso gabashi da arewa maso yammacin kasar, galibin an kaddamar da hare-haren ne a wasu kauyuka dake makwabtaka da juna.
Sama da mutane 50 ne aka hallaka a hare-haren da masu dauke da makamai suka kaddamar a wasu yankunan dake kan iyakokin jahohin Adamawa da Taraba, 'yar majalisar jihar Adamawa Sodomti Tayedi, ta tabbatar da hakan ga manema labarai.
Ta ce sakamakon wasu hare-hare a yankunan karamar hukumar Numan, yankin da take wakilta a majalisar dokokin jihar, mazauna yankunan wadanda galibinsu manoma ne sun tsere daga yankunan, sun bar gonakinsu.
A wani labarin makamancin wannan, hukumar bada agajin gaggawa ta kasa ta ce a kalla an samu gawarwakin mutane 26 sakamakon wasu hare-hare da aka kaddamar a cikin kwanaki biyu wadanda ake zargin barayin shanu ne suka kaddamar a jihar Sokoto dake arewa maso yammacin kasar.
Mazauna yankin sun tabbatar da cewa an yi awon gaba da shanu masu yawa kana an kona gidaje a lokacin da maharan suka afkawa kauyen Gandi a yankin Rabah da yammacin ranar Litinin. (Ahmad Fagam)