Shugaban hukumar Ibrahim Dingyadi, ya ce an ceto mutane 8 a hatsarin da ya auku sanadiyyar kifewar kwale-kwale a ranar Asabar da ta gabata.
Ibrahim Dingyadi, ya shaidawa manema labarai cewa, al'amarin ya auku ne a lokacin da kwale-kwalen mai fasinjoji 30 ya kife a kan hanyarsa ta zuwa kogin Bafarawa na jihar.
Ya kara da cewa an umurci masu linkayar da su nemo ragowar mutanen 21.
Yanzu haka dai, kogin Bafarawa, inda hatsarin ya auku, na matsayin koli saboda yanayin damina da ake cikin a Nijeriya. (Fa'iza Mustapha)