in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Minister: Najeriya zata yi koyi da kasar Sin wajen zuba jari mai yawa a fannin kimiyya da fasaha
2018-07-10 10:01:21 cri
Ministan kimiyya da fasaha na Najeriya Ogbonnaya Onu yace gwamnatin kasar za ta yi koyi da dabarun kasar Sin wajen zuba jari mai dunbun yawa a fannin sabbin fashohin zamani domin samun saurin bunkasuwa.

Ministan ya fadawa 'yan jaridu a Legas, birnin kasuwancin kasar cewa, kasar Sin ta yi amfani da fasaha wajen ciyar da biliyoyin jama'ar kasar, ta samar da arziki kuma ta bude kofar tattalin arzikinta ga duniya.

Jami'in ya furta hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi game da dokar da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sanyawa hannu a ranar 5 ga watan Fabrairu wadda zata tabbatar da bunkasa fannin kimiyya da fasaha domin ciyar da kasar gaba daga dukkan fannoni.

Manufar dokar shi ne, ba da fifiko ga kishin kasa a matsayin hanyar da kasar Sin ta yi amfani da shi wajen gina kasarta, Onu ya kara da cewa, dokar za ta sauya fasalin tattalin arzikin Najeriyar daga yanayin na rashin tabbas, da yin amfani da albarkatu a cikin gida don samun dauwamamman cigaba, da kuma yin amfani da ilmin fasaha wajen bunkasa cigaban kasar. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China