in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Buhari Ya Nemi Da A Sadaukar Wurin Yakar Cin Hanci Da Rashawa
2018-07-09 20:09:42 cri

Mun samu labari daga shafin Intanat na Leadership a yau cewa, Shugaba Muhammadu Buhari, ya bukaci 'yan Nijeriya da su ci gaba da baiwa yakin da gwamnatinsa ke yi da cin hanci da rashawa hadin kai, domin ci gaban Nijeriya.

Buhari, ya yi wannan kiran ne a Abuja ranar Asabar wajen kaddamar da wasu littafai biyu, wadanda tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha, Manjo Janar Sam Momoh, mai ritaya, ya rubuta su. Kamfanin Dillancin labarai na kasa (NAN), ya kawo rahoton littafan biyu, "Restructuring Nigeria beyond Oil'', da "Pulling Nigeria off the Brink'' an kaddamar da su ne ga al'umma domin bukin cikar marubucin shekaru 75 a duniya.

Buhari ya ce, a rubututtukan marubucin littafan na baya, ya nuna mahimmancin yakar cin hanci da rashawa, domin daukaka matsayi da ci gaban Nijeriya. Shugaban, wanda babban sakataren hukumar ilimi ta, 'Universal Basic Education Commission (UBEC), Dakta Hamid Bobboyi, ya wakilce shi ya ce, ya wajaba ga dukkanin 'yan Nijeriya da su baiwa wannan yakin da ake yi goyon baya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China