Sunday Adeleye, darakta a hukumar AFN, ya shaidawa manema labarai cewa, matakin ya biyo bayan wani taron gaggawa da kwamitin gudanarwar hukumar ya yi game da zanga-zangar.
An bude gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsallen da aka shirya zai dauki kwanaki 3 ne a ranar Asabar a filin wasanni na Abuja, inda 'yan wasan da za su wakilci Nijeriya a gasar wasanni guje-guje da tsalle-tsalle ta nahiyar Afrika za su yi gwaji.
Birnin Asaba na jihar Delta ne zai karbi bakuncin gasar a watan Augusta mai zuwa.
Da farko, 'yan wasan sun rufe hanyoyin wasa a filin na Abuja, inda suke bukatar ganawa da kwamitin gudanarwa AFN domin magance rashin kyan yanayin walwalarsu da kuma gazawa wajen biyan kudinsu na alawus-alawus.
Wasu daga cikinsu sun kuma koka da kyan yanayin walwalarsu a lokacin da suke wasanni a duk wata gasa da hukumar ta shirya.
Sun kuma soki wakilinsu a kwamitin gudanarwar hukumar da gazawa wajen kare muradunsu yadda ya kamata. (Fa'iza Mustapha)