in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban sifeton 'yan sandan Najeriya: Ku kasance cikin shirin ko-ta-kwana
2018-07-09 19:57:10 cri

Mun samu labari daga shafin Intanat na Leadership a yau cewa, babban sifeton 'yan sanda na tarayyar Najeriya Ibrahim Idris, ya umurci dukkanin kwamishinonin 'yan sanda na jihohin kasar, da mataimakansa na sassan kasar, gami da dukkanin rundunonin 'yan sanda na Najeriya, da su kasance a cikin shirin ko-ta-kwana, ba tare da wani bata lokaci ba, domin magance duk wasu ayyukan laifi a jihohinsu.

Wannan umurnin ya biyo bayan wani kwantan bauna, da wasu da ake jin gungun 'yan fashi ne suka yi wa wasu jami'an 'yan sandan kasar, inda har suka kashe jami'ai bakwai daga cikinsu, a sha tale talen unguwar Galadimawa, da ke babban birnin tarayyar kasar Abuja, a ranar 2 ga watan Yuli nan.

Inda nan take, shugaban 'yan sandan na kasa a ranar 3 ga watan na Yuli, ya kafa wani kwamitin kwararru na 'yan sanda, wanda zai binciki harin na kwantan bauna da aka kaiwa jami'an na 'yan sandan, wanda a yanzun haka, har kwamitin ya kai ga kama mutane biyar da ake jin suna da alaka da kisan.

Kakakin rundunar na kasa, Jimoh Moshood, cikin sanarwar da ya fitar jiya da daddare cewa ya yi, "Akwai bukatar a karfafa tsaro a duk sassan kasar, domin tsare rayuka da dukiyoyin al'umma."

A yanzun haka, dukkanin mataimakan shugaban 'yan sanda na kasa, masu jagorantar rundunonin sassa, da kwamishinonin 'yan sanda na Jihohi, shugaban 'yan sanda na kasa ya ba su umurni mai karfi, da su karfafa tsaro da kuma fitar da sabbin dubarunsu na hana aikata ayyukan laifi, ta hanyar samar da isassun jami'an tsaro da kayan aikinsu a dukkanin wuraren da batagari suke. "Musamman su fi mayar da hankali a wuraren ibada, makarantu, kasuwanni da wuraren shakatawa domin hana aikata wani ta'addanci. Su kuma dage wajen ci gaba da kai hare-hare a duk wuraren da aka sani maboyan masu laifi ne."

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China