Jirgin kasan na kasar Sin mai saurin tafiya yana tafiyar kilomita 350 ne a kowace sa'a, a lokacin da jirgin na Fuxing ya fara zirga zirga tsakanin Beijing da Shanghai a ranar 21 ga watan Satumbar 2017.
CRRC ta shirya tsab domin samar da jiragen kasan masu tsananin gudu, don gudanar da zirga zirga tsakanin biranen kasar, kana tana kokarin fadada shirin domin samar da jiragen ga kasuwannin duniya. (Ahmad Fagam)