in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta harba sabon tauraron dan Adam mai bibiyar yanayin muhalli
2018-05-09 10:22:34 cri

Kasar Sin ta harba sabon tauraron dan Adam na Gaofen-5, mai daukar hoto da bada bayanan dukkan launi da abubuwan dake kunshe cikin hoton, a wani bangare na aikin da kasar ke yi na samun ingantattun hotunan nazarin yanayin kasa.

An harba tauraron Gaofen ne bisa amfani da rokar Long Maarch 4C da misalin karfe 2 da minti 28 na sanyin safiyar yau Laraba, agogon birnin Beijing, daga cibiyar harbar tauraron dan Adam ta Taiyuan dake lardin Shanxi na arewacin kasar Sin. Wannan, shi ne karo na 274 da rokar Long March ya harba tauraron dan Adam.

Za a iya yin amfani da tauraron ne wajen samun cikakkun bayanan bibbiyar yanayin muhalli.

Hukumar kimiyya da fasaha mai kera fasahohin da ake harba sararin samaniya ta kasar Sin ce ta tsara tare da kera Tauraron Gaofen-5 wanda aka tsara zai yi aiki tsawon shekaru 8.

A cewar babban jami'in da ya tsara jerin taurarin Gaofen, Gaofen 5, shi ne irinsa na farko da kasar Sin ta samar, wanda zai bibbiyi gurbutar iska. Zai iya bayyana yanayin gurbatar iska a kasar Sin ta hanyar sa ido kan abubuwan dake gurbata iskar da hayaki mai gurbata muhalli da masana'antu ke fitarwa.

Gaofen-5 shi ne tauraron dan Adam na farko a duniya, wanda zai yi cikakken nazari kan yanayin sararin samaniya da kuma yankin kasa.

A cewar Wang Qiao, Jami'i a ma'aikatar kiyaye muhalli na kasar Sin, tauraron zai iya gano wureren taruwar ruwa na dindindin da muhallin yankin kasa da sinadarai, ta yadda zai bada gamsassun bayanai, domin bibbiyar muhalli a kasar Sin da lalubo albarkatu da kare aukuwar iftila'i. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China