Mai magana da yawun hukumar Li Guoping ya bayyana cewa, yanzu haka aikin harba tauraron dan Adam din da wasu na'urorin hangen nesa wadda cibiyar nazarin fasahar kere-kere dake Harbin ta tsara ya yi nisa, ana kuma sa ran harba su ne tare da Longjiang-1 da Longjiang-2 cikin sararin samaniya.
Bayanai na nuna cewa, Chang'e-4 zai yi dakon na'urorin kasashen Jamus, Netherlands, Saudiya da kuma Sweden. (Ibrahim Yaya)