in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Afrika ta kudu ya gana da Wang Yi
2018-06-04 15:52:10 cri

Jiya 3 ga wata, shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa, ya gana da ministan harkokin waje na kasar Sin Wang Yi a birnin Pretoria.

Yayin ganawar tasu, Cyril Ramaphosa ya bayyana cewa, Afrika ta kudu na bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare, kuma yana fatan kara hadin kai da kasar Sin bisa yanayin da duniya ke ciki a halin yanzu mai cike da sauye-sauye. Ban da wannan kuma, Afrika ta kudu na maraba da zuwan shugaba Xi Jinping, don halartar taron shugabanin BRICS da za a yi a watan Yuli, da ziyarar da zai yi a Afrika ta kudu. Ya kara da cewa, Afrika ta kudu za ta ci gaba da nace ga manufar kasar Sin daya tilo, kuma a matsayin kasar babbar bakuwa daya tilo daga Afrika, Afrika ta kudu na farin ciki sosai da shirin halartar bikin baje koli na shige da fice na kasa da kasa karo na farko da za a gudanar a watan Nuwamba a birnin Shanghai.

A nasa bangare kuwa, Mista Wang ya ce, tsarin mulkin na gurguzu mai hayalayyar musamman ta kasar Sin ya shiga sabon zamani da ake ciki, kuma bunkasuwar Afrika ta kudu ita ma ta shiga sabon zamani, hakan ya sa dangantakar kasashen biyu na fuskantar zarafi mai kyau. Ya ce ya kamata bangarorin biyu sun kara sulhuntawa, da kara amincewa da juna bisa manyan tsare-tsare, da kuma zurfafa hadin kai da kawo moriyar juna. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China