Wang Yi ya ce kasar Sin za ta sanya kokari tare da kungiyar EU wajen tabbatar da yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran a dukkan fannoni.
Wang Yi ya kuma amsa tambayoyi tare da wakiliyar kungiyar EU Federica Mogherin game da batun nukiliyar kasar Iran, inda ya bayyana cewa, ya kamata a yi shawarwari cikin adalci, da tattauna sauyin yanayin da ake ciki da sabbin matsalolin da ake son lura da su tare, bisa yanayin ci gaba da tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar batun nukiliyar Iran a dukkan fannoni. (Zainab)