Li ya yi wannan kiran ne a yayin da ya halarci taron hadin gwiwar shugabannin Sin da kasashen tsakiya da gabashin Turai wato China-CEEC karo na 7 a birnin Sofia, na kasar Bulgaria, inda ya yi maraba da bude kofa, da yin cudanya tare karkashin tsarin na 16+1 don samun nasarori masu tarin yawa karkashin hadin gwiwar bangarorin biyu.
Ya ce tsarin hadin gwiwar Sin da Turai ya kasance wani muhimmin tushe wanda zai kara karfafa amincewa da juna da cin moriyar juna daga dukkan bangarorin da abin ya shafa, kana zai taimaka wajen bunkasa ci gaban dangantakar dake tsakanin Sin da Turai. (Ahmad Fagam)