in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya isa Indonesia
2018-05-06 21:04:20 cri
A yammacin ranar Lahadi, bisa agogon wurin, firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya isa Jakarta, fadar mulkin kasar Indonesia, inda ya fara ziyara a kasar.

Bayan da ya sauka daga jirgi, mista Li ya fadi cewa, bana ita ce shekara ta 5 bayan da Sin da Indonesia suka kulla abokantakar da ta shafi manyan tsare-tsare. A cewarsa, ziyararsa a wannan karo na da nufin zurfafa amincewa da juna, da hadin gwiwa, da kara dankon zumuncin dake tsakanin jama'ar kasashen 2.

Babban jami'in kasar ya kai ziyarar ne bisa gayyatar shugaban kasar Indonesia Joko Widodo.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China