in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya tashi zuwa Bulgaria da Jamus
2018-07-05 13:21:08 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya tashi daga birnin Beijing a Alhamis din nan, a kan hanyar sa ta zuwa kasashen Bulgaria da Jamus domin gudanar da ziyarar aiki.

Li zai kuma halarci taro karo na 7, na hadin gwiwar jagororin Sin, da na tsakiya da gabashin kasashen Turai ko CEEC a takaice, taron da za a gudanar a birnin Sofia. Kaza lika zai jagoranci taron tattaunawa karo na biyar, na jami'an kasar Sin da na Jamus.

Mr. Li zai ziyarci Bulgaria da Jamus ne, bisa gayyatar da ya samu daga firaministan Bulgaria Boyko Borissov, da kuma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China