Firaminista Li ya jaddada cewa, yayin ziyararsa Japan a wannan karo, shi da shugaban Japan sun yi waiwaye adon tafiya da takaita nasarorin da suka samu a baya, da cimma matsaya tsakaninsu, kan yadda za a raya huldar kasashen biyu cikin dogon lokaci kuma ta hanyar da ta dace. Suna ganin cewa, akwai sabbin damarmaki wajen kyautata dangantakar Sin da Japan. Firaministan ya ce ya kamata bangarorin biyu su nuna himma da kwazo wajen daukar sabbin matakan inganta huldarsu, da kyautata burin jama'arsu gami da kasashen duniya, kan ci gaban dangantakarsu.
A nasa jawabin kuma, Shinzo Abe ya ce, ziyarar firaministan kasar Sin Li Keqiang a Japan, ta sake maido da dangantakar kasashen biyu kan turba madaidaiciya. Inda ya ce ya kamata kasashen biyu su yi kokari kafada da kafada don warware matsalolin dake gabansu.(Murtala Zhang)