Li Keqiang ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi ga taro kan kasuwanci karo na 8, da aka yi tsakanin kasar Sin da kasashen tsakiya da gabashin Turai a birnin Sofia na Bulgaria.
Ya ce tattalin arzikin kasar Sin ya ci gaba da samun ingantuwa cikin matsakaicin mataki da sama da kaso 7 cikin dari a shekaru 5 da suka gabata, kuma yana bada gudummawar sama da kaso 30 cikin dari ga ci gaban tattalin arzikin duniya a duk shekara.
Har ila yau, ya ce ma'aunin tattalin arziki wato GDP na kasar Sin, ya karu da kaso 6.8 cikin dari a rubu'in farko na bana, wanda ya dara na makamancin lokacin a shekarun da suka shude.
Firaministan ya kuma jadadda matsayar kasar Sin, na tsayawa kan manufar sauya fasalin kasuwarta da kara bude kofa. (Fa'iza Mustapha)