in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta Kudu ta ce ana samun nasara a tattaunawar sulhu da ake a Khartoum
2018-07-07 15:33:39 cri
Gwamnatin Sudan ta kudu, ta ce ana samun nasara a tattaunawar sulhu da ake tsakaninta da bangarorin adawa, tana mai fatan za a cimma matsaya nan ba da jimawa ba, yayin da ake ci gaba da tattaunawar a Khartoum, babban birnin Sudan.

Mukaddashin Ministan harkokin wajen Sudan ta Kudu, Martin Elia Lomuro, ya shaidawa manema labarai cewa, bangarori masu adawa da juna, sun samu ci gaba kan daftarin da ya kunshi yarjejeniyar tsaro, kuma mai yiyuwa a rattaba hannu kansa cikin kwanaki kalilan masu zuwa.

Ya kara da cewa, sun tabbatarwa bangaren zartaswar kasar cewa, ana cimma nasarori, kuma suna jin dadin yadda tattaunawar ke gudana.

A makon da ya gabata ne Shugaba Salva Kirr da jagoran 'yan adawa Riek Machar, suka rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita rikici, tare da alkawarin kawo karshen fadan da aka shafe shekaru 4 ana yi a kasar.

Sai dai kuma yarjejeniyar ta rushe sa'o'i bayan ta fara aiki, inda bangarorin ke nuna yatsa ga juna.

Sudan na ci gaba da shiga tsakani karkashin yunkurin kungiyar raya yankin gabashin Afrika ta IGAD, a kokarin samar da mafita a siyasance game da rikicin Sudan ta kudu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China