in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Sudan ta kudu sun sanar da rasuwar fararen hula 16 sakamakon watsi da tsagaita wuta
2018-07-02 13:39:12 cri
Dakarun sojojin gwamnatin Sudan ta kudu, sun sanar da rasuwar fararen hula 16, sakamakon watsi da aka yi da yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin tsagin gwamnati da na 'yan adawar kasar.

Kakakin rundunar SPLA Lul Ruai Koan, ya ce baya ga wadanda suka rasa rayukansu a baya bayan nan, wasu karin mutane 22 sun jikkata, ciki hadda baki 'yan kasashen waje.

Lul Ruai Koan wanda ya shaidawa kamfanin dillancin larabai na Xinhua hakan ta wayar tarho, ya ce a ranar Asabar, dakarun dake biyayya ga jagoran 'yan adawar kasar Riek Machar, sun kaiwa sojojin gwamnati hari a kudanci da arewacin Liech, dake tsohuwar jihar Unity.

Kaza lika a arewacin jihar Upper Nile ma, dakarun 'yan adawar sun kaddamar da hari kan wani garken shanu dake gundumar Maban, lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwar mutane 16, tare da jikkatar karin wasu mutanen 22, kana aka sace wasu dabbobi masu tarin yawa.

Kakakin bangaren gwamnatin ya ce an keta hurumin yarjejeniyar da aka kulla tsakanin sassan biyu, sa'o'i bayan da shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakin sa, kuma jagoran 'yan adawar kasar Riek Machar suka ba da umarnin fara aiwatar da ita.

Cikin wadanda suka rasa rayukan su yayin hare haren dai hadda wasu 'yan kasar Habasha 3 dake hada hadar kasuwanci a Sudan ta kudun, a daidai gabar da tsagin 'yan adawar kasar ke neman iko da wasu karin yankunan kasar, kafin su amince da fara aiwatar da 'yarjejeniyar daga ranar Lahadi, kamar dai yadda Lul Ruai Koan ya bayyana. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China