Wakilin Sakatare Janar na MDD kuma shugaban shirin UNMISS David Shearer, ya ce yarjejeniyar da aka cimma a Khartoum ranar Laraba da ta gabata, ya bude wani sabon babi kuma ya karfafawa shirin gwiwa.
David Shearer ya shaidawa manema labarai a birnin Juba cewa, a ganinsa, yarjejeniyar wani yunkuri ne na ci gaba, sannan mafari ne na samar da cikakkiyar yarjejeniyar zaman lafiya mai dorewa, wadda za a tattauna kanta cikin makonni masu zuwa.
Ya kuma yi kira ga bangarorin dake fada da juna, su sake shiga yarjejeniyar, ya na mai cewa babu yadda za a yi a wanzar da zaman lafiya a lokacin da ake tsaka da rikici a kasa.
Ya kara da cewa, idan bangarori masu fada za su kara kokari akan yarjejeniyar tsagaita bude wutan domin tabbatar da ya yi aiki, to akwai dama da masu ruwa da tsaki ke ganin za a zauna don nazarin sauran batutuwa. (Fa'iza Msutapha)