Jami'in na MDD wanda ya bayyana hakan ta hannun kakakinsa Stephane Dujarric, ya ce ya gamsu da aniyar bangarorin da abin ya shafa na ci gaba da sasantawa. A don haka ya bukaci dukkan bangarorin da abin ya shafa da su nuna halin ya kamata na ganin sun kai ga cimma yarjejeniya a kan batutuwan da ba a kai ga cimmawa ba a fannonin shugabanci da ma matakan tsaro.
Ya ce, a shirye MDD da kungiyoyin IGAD da AU suke na goyon bayan gwamnati da al'ummar Sudan ta kudu, wajen ganin an aiwatar da yarjejeniyar da kowa ne bangaren zai yin na'am da ita.
Tun a ranar Larabar da ta gabata ce dai shugaban Sudan ta kudu Salva Kiir da jagoran 'yan adawar kasar Riek Machar suka amince da tsagaita bude wuta na din-din-din, wadda za ta fara cikin sa'o'i 72, lamarin da ake fatan zai kawo karshen rikicin shekaru da rabi da ya addabi kasar.(Ibrahim)