Guterres wanda ya bayyana cikin wata sanarwa ta hannun kakakinsa Stepahane Dujarric, ya kuma mika sakon ta'aziyya ga gwamnatin Bangaladesh da iyalan wadanda harin ya rutsa da shi.
Jami'in na MDD ya sake nanata cewa, kaiwa ma'aikatan wanzar da zaman lafiya na MDD hari na iya zama laifi na yaki. Ya kuma nanata goyon bayansa ga ma'aikata maza da mata dake aiki karkashin laimar MDD a kasar Sudan ta kudu, a kokarin da suke yi na kare rayukan fararen hula da ma tabbatar da zaman lafiya a kasar da yaki ya wargaza.
A jiya ne dai aka halaka wani ma'aikacin wanzar da zaman lafiya na MDD dan kasar Bangaladesh a wani harin da aka kaiwa tawagar su da ke samar da kariya ga ma'aikatan bayar da agajin jin kai ga al'ummomin dake tsakiyar yankin Equatoria na kasar Sudan ta kudu. (Ibrahim)