Salva Kiir tare da Riek Machar sun cimma yarjejeniyar dakatar da bude wuta ne, yayin tattaunawar sulhu da suka gudanar a birnin Khartoum na kasar Sudan.
A ranar Alhamis ne dai shugaba Kiir ya ba da umarnin ta kafar radiyon kasarsa, inda ya yi kira ga dakarun sojin gwamnati da su kasance cikin shirin ko ta kwana, kuma kada su kaddamar da wani hari, har sai idan an auka musu. Kaza lika ya umarce su da su baiwa masu aikin jin kai dukkanin dama, ta gudanar da ayyukan su ba tare da wani tarnaki ba. (Saminu Hassan)