Majisar gudanarwar kasar Sin ta bukaci a hanzarta karfafa matakan aiwatar da sabbin nau'o'in cinikayyar amfanin gona a fadin kasar.
A wata sanarwa da majalisar ta fitar bayan zamanta na ranar Laraba, wanda firaiministan kasar Li Keqiang ya jagoranta, sanarwar tace, za'a kaddamar da wasu shirye shirye wadanda zasu kara taimakawa harkokin cinikayya wanda hakan zai bunkasa masana'antun kasar masu yawa, kuma zai shafi dabarun amfani da hanyoyin internet a kasar.
Sanarwar tace, za'a fara wani shirin bada horo wanda zai samar da wasu sabbin nau'o'in kwararrun manoma da za su dukufa a kan masana'antu da kirkire-kirkire a yankunan karkara da nufin tsame al'ummar yankuna masu yawa daga kangin fatara.
Majalsiar ta kuma yi alkawarin samar da wasu tsare tsare na musamman a fannin kudi, da haraji, da filyen noma da kuma makamashi da nufin karfafa gwiwa a fannonin ciniki da kuma sarrafa kayan amfanin gona.
A cewar sanarwar, za'a kirkiro wani tsarin samar da kudade wadanda za'a yi amfani dasu wajen karbar hayar manyan injina da motocin aikin gona.(Ahmad)