A jiya Lahadi da dare ne, gwamnatin kasar Sin ta gabatar da takardarta ta farko da ke kunshe da wasu shawarwari, game da yadda za a aiwatar da gyare-gyare a fannin aikin gona, ta yadda za a bunkasa ayyukan gona da raya kauyuka, inda aka bayyana cewa, za a bunkasa aikin gona ta hanyar inganta amfanin gona. Tang Renjian ya bayyana cewa, an gabatar da shawarwari hudu game da wannan batu.
Na farko, akwai bukatar canja tsarin raya aikin gona. A cikin takardar, an ba da muhimmanci ga batun inganci, da kiyaye muhalli, inda aka bukaci da a canja tsarin yin amfani da albarkatun halittu zuwa raya aikin gona da samun bunkasuwa mai dorewa ba tare da gurbata yanayi ba.
Na biyu, a zurfafa manufofin raya aikin gona bisa ma'auni. A kyautata tsarin ma'aunin yanayin samar da jigilar kayayyakin amfanin gona, ta yadda zai dace da ma'aunin kasashe masu ci gaba.
Na uku, a yi amfani da hanyar samar da kayayyaki ba tare da gurbata muhalli ba. Ya kamata a kara kiyaye muhalli a wuraren samar da kayayyakin amfanin gona, da rage yawan amfani da maganin kashe kwari masu illa ga bil-Adam.
Na hudu, a kyautata tsarin sa ido ga ingancin amfanin gona da tsaron abinci. (Zainab)