in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta aiwatar da shirin sauya takin zamani
2017-06-15 09:06:28 cri

A ranar Laraba ma'aikatar aikin gona ta kasar Sin ta kaddamar da wani shiri na sauya takin zamani mai dauke da sinadarai inda za ta maye gurbinsa da takin gargajiya a gundumomi da yankuna 100 na kasar.

Mataimakin ministan aikin gona na kasar Sin Yu Xinrong, ya bayyana cewa, gwamnatin tsakiya ce za ta samar da kudaden shirin sauya takin zamanin wanda zai shafi noman ganyen shayi, ganyaye, da kayan marmari.

Ya ce, karkashin wannan shirin, gwamnati za ta baiwa manoma rangwame wadanda suke amfani da takin gargajiya domin ba su kwarin gwiwa domin rungumar shirin gadan-gadan, Yu ya bayyana hakan ne a lokacin taron aiwatar da shirin a lardin Hubei dake tsakiyar kasar Sin.

A shekarar da ta gabata, kasar Sin ta yi amfani da takin zamani, amma ba'a samu wata karuwa ba a karon farko tun bayan da Sin ta aiwatar da shirinta na yin garam-bawul da bude kofa, in ji mataimakin ministan.

Har yanzu, ana samun matsaloli na rashin inganci a kayan marmari, ganyaye da kuma ganyen shayi da ake nomawa saboda yawan sinadaran da ake amfani da su wajen noma su. Don haka shirin sauya takin zamanin ya zama tilas domin samar da kayan amfanin gona masu inganci.

A bisa ga wani shiri na kasar Sin, za'a rage yin amfani da sinadaran takin zamani da ake amfani da su da kashi 20 bisa dari nan da shekarar 2020, wajen noma amfanin gona da suka hada da kayan marmari, ganyaye, da ganyen shayi.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China