in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Beijing: manoma kimanin dubu 415 suna aikin gona
2018-01-31 11:05:40 cri

Kwanan baya ne hukumar kididdiga ta birnin Beijing da kuma sashen bincike na birnin karkashin shugabancin hukumar kididdiga ta kasar Sin suka kaddamar da sakamakon binciken aikin gona na birnin Beijing karo na 3. Binciken da ya nuna cewa, yanzu haka akwai manoma mazauna birnin Beijing kimanin dubu 415 dake gudanar da aikin gona.

Alkaluman kididdigar da aka fitar sun kuma nuna cewa, kudin shiga da birnin ya samu daga harkokin yawon shakatawa a yankunan karkara da dai sauransu ya karu sosai, wanda yawansa ya kai kudin Sin RMB yuan biliyan 15.07. Mutane kimanin miliyan 200 ne suka ziyarci kauyukan birnin, a cewar rahoton. Kana ingantuwar aikin gona ya kara kyautata gidajen manoma. A shekarar 2016, yawan iyalan manoman da suka mallaki gidaje a nan Beijing ya kai miliyan 1 da dubu 17, wanda ya kai kashi 98.5 cikin dari bisa jimillar dukkan iyalan manoman birnin. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China