Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar a ranar 8 ga watan Mayu cewa, kasar Amurka ta janye daga yarjejeniyar batun nukiliya na kasar Iran, tare da sake sakawa kasar Iran din takunkumin da aka soke shi domin yarjejeniyar batun nukiliyar. Kasar ta Iran ta bayyana cewa, za ta kiyaye bin yarjejeniyar a wannan lokaci tare da yin shawarwari da sauran bangarorin da suka daddale yarjejeniyar, amma idan ba a tabbatar da moriyar kasar Iran da aka kayyade a cikin yarjejeniyar ba, hukumar makamashin nukiliya ta kasar Iran zata sake gudanar da aikin tace sinadarin Uranium. (Zainab)