in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Khamenei na neman a kara karfin tace uranium a Iran
2018-06-05 10:47:42 cri

Gidan telibijin mallakar kasar Iran, ta ba da labari a jiya 4 ga wata cewa, shugaban addini na kasar Iran Ayatollah Sayyed Ali Khamenei, ya ba da umurni a wani taron da aka yi a wannan rana, game da bukatar hukumar makamashin nukiliya ta Iran da ta kara karfinta na tace ma'adanin uranium.

An ba da labari cewa, a watan Yuli na shekarar 2015, kasashe shida masu ruwa da tsaki kan batun nukiliyar kasar Iran wato Amurka, Birtaniya, Faransa, Rasha, Sin da Jamus sun kai ga cimma matsaya wajen daidaita wannan matsala a dukkanin fannoni.

Bisa yarjejeniyar da aka cimma, Iran ta yi alkawarin kayyade shirinta na bunkasa makaman nukiliya, a sa'i daya kuma tana da ikon yin amfani da makamashin nukiliya cikin lumana, matakin da ya sanya kasashen duniya soke takunkumin da suka sakawa kasar ta Iran. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China