in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Javad Zarif ya bukaci kasashen duniya su yi Allah wadai da janyewar Amurka daga yarjejeniyar Nukiliyar Iran
2018-06-04 10:56:16 cri
Ministan harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif, ya yi kira ga gamayyar kasashen duniya, da su yi Allah wadai da janyewar Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar kasar sa.

Cikin wasu wasiku da ya aikewa takwarorin sa na wasu kasashen duniya da dama, Mr. Zarif ya yi gargadi game da mummunan tasirin da janyewar Amurka daga yarjejeniyar ta JCPOA zai haifar. Matakin da a cewar sa ya sabawa doka, kuma Amurka ta dauke shi ne bisa radin kan ta kadai.

Ya ce "janyewar Amurka daga wannan yarjejeniya ya sabawa ka'ida, ya kuma haifar da kalubale ga kudurorin MDD, tare da yiwa manufofin ayyukan hadin gwiwa na kasa da kasa karan-tsaye".

Mr. Zarif ya kara da cewa, matakin na Amurka shi ne mafi girma da mahukuntan ta suka dauka, domin ganin sun karya lagon kudurin MDD mai lamba 2231, wanda aka cimma a watan Yulin shekarar 2015, ya kuma kai ga haifar da nasarar amincewa da yarjejeniyar ta JCPOA.

Ministan na Iran ya ce, yarjejeniyar ta kawo karshen nunawa juna yatsa maras amfani wanda aka shafe kusan shekaru 10 ana yiwa juna, tsakanin kasashe masu ruwa da tsaki kan batun nukiliyar Iran. Kuma wannan yarjejeniya ta samar da cikakkiyar dama, ta cimma matsaya guda mai ma'ana tsakanin dukkanin sassa, wanda hakan ke nuna cewa, ba za a taba yarda da sauya ta, ko hawa teburin shawarwari don sake mata wani gyaran fuska ba. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China