in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Isra'ila: Burin ziyararsa a Turai shi ne hana shirin nukiliya na Iran
2018-06-04 10:47:11 cri
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana a gun wani taron majalisar ministoci da aka yi a jiya 3 ga wata cewa, zai kai ziyara a Turai tare da yin shawarwari da shugabannin Jamus, Faransa da Birtaniya don hana a aiwatar da shirin nukiliya na Iran.

A cewarsa, zai gudanar da ziyara a ranar 4 ga wata, inda zai gana da shugabar gwamnatin Jamus Angela Dorothea Merkel, da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, da firaministar Birtaniya Teresa May, don tattauna halin da yankin gabas ta tsakiya ke ciki, musamman ma batun Iran.

Yayin ganawar tasu, Netayahu zai nanatawa kasashen uku cewa, ko kadan Isra'ila ba za ta amince da Iran ta dauki makaman samar da nukiliya ba. Ban da wannan kuma, yadda za a hana Iran ta habaka karfinta a yankin gabas ta tsakiya musamman ma a kasar Sham, zai zama muhimmin batu a yayin ganawar tasu ta wannan karo. Kaza lika Isra'ila za ta ci gaba da dakile ayyukan soja da Iran ke gudanarwa a Sham.

A daya bangaren kuma, ministan harkokin wajen kasar Sham Walid Muallem ya bayyana a 2 ga wata cewa, abubuwan da Iran ta girka a Sham na bisa bukatun gwamnatin Sham ne, kuma babu wasu na'urori ko sojojin da Iran ta girka a Sham. Sai dai akwai mai ba da shawara kan harkokin soja na Iran da ke tallafawa kasar ta Sham. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China